Wani Dan Kasuwa Ya Rushe Katafaren Gidan Da Ya Gina Wa Budurwarsa Saboda Ta Rabu Da Shi

Budurwar ta rabu da matashin dan kasuwar ne bayan ya gina matan wani bene na gani na fada a filin da ake cewa mallakinta ne.

Rabuwar budurwar da shi ke da wuya sai ta sa gidan a kasuwa inda ta shiga shafukan zumnata tana talla tare da neman mai saye.

Kafin ciniki ya kaya sai mutumin ya dauko hayar buldoza kuma ba tare da bata lokaci ba ta fara ruguza benen da tsakar rana.

Bidiyon lamarin da ya faru a kasar Afirka ta Kudu da taken  ya yi tashe a Twitter inda mutane ke ta tofa albarkacin bakinsu game da matakin da matashin ya dauka.

Ra’ayoyi sun bambanta tsakanin masu cewa abin da ya aikata shi ne daidai da yaudarar da budurwar ta yi masa. 

Akwai kuma na cewa duk ma abin da ya yi shi ne da asara; wasu kuma na ganin idan budurwar ta kai kara kotu za ta yi nasara.

-Rahoton Aminiya

Post a Comment

0 Comments