Wasu Manyan Nijeriya Ne Suka Kirkiri ‘Yan Ta’addan Kasar- Mailafia

Obadia Mailafia

Daga Muhammad Farouk

Tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana cewa bai kamata ana yafewa ‘yan bindiga ba, saboda ba abin da suke yi sai cutar da al’umma kamar yadda Jaridar Punch ta labarto. 

Obadiah Mailafia ya ce; “a lokacin zaben 2015, sun kawo bakin haure zuwa kasarnan, suka ba su makamai, sun yi hakan ne idan Goodluck Jonathan ya ki mika wuya (idan ya fadi zabe), za a yi yaki. Sun shirya tsaf domin yakin basasa; ba su yarda a zauna lafiya ba”, inji shi. 

Ya ci gaba da cewa; “tabbas Jonathan sai ya mika musu mulki, sai suka juyawa ‘yan bindigar baya, su kuma ‘yan bindigar sai suka ce musu; ‘ba ku isa ba, ku kuka kawo mu, kuma muna nan a nan”, ya tabbatar. 

 “akwai wadansu manyan kasashe da suke son tarwatsa kasarnan. Shi ne abin da na yi imani da shi. Akwai wata babban kontena ta mota cike da makamai da aka kawo daga Turkiyya, akwai lokacin da aka kawo daga Iran. Amma ba wanda ya yi bincike daga nan, aka watsar da komai, aka rufe zancen”, ya lurantar. 

Mailafia ya yi kira ga wadanda suke hada tsagerun Neja Delta da sauran ‘yan ta’addan kasar da suke da muggan makamai, inda ya ce; “ban yarda a rika hada tsagerun Neja Delta da ‘yan ta’adda ba. Wadannan mutanen (‘yan ta’adda) ba ma kawai ‘yan bindiga bane. Dan bindiga kamar barawo yake. ‘agbero’ ana iya kiransu da ‘yan bindiga. Amma wadannan mutanen suna dauke da muggan makamai da rokoki ba za a kira su da ‘yan bindiga ba. Kawai ‘yan ta’adda ne”, ya tabbatar. 

Ya ci gaba da cewa; “sun kashe, sun yi kisan kiyashi, sun yi fyade, sun tarwatsa garuruwa”, inji shi. 

Sai dai Mailafia bai gabatar da wata kwakkwaran hujja kan zantukan da ya yi ba. Domin ya saba irin wadannan zantuka ba tare da gabatar da wata hujja ba. 

Idan mai karatu bai manta ba, a watan Agustan 2020, Hukumar tsaro ta DSS ta garkame Mailafia bisa ikirarin da ya yin a cewa; wani gwamna daga arewacin Nijeriya shi ne shugaban Boko Haram. 

Bayan fitowarsa daga wurin DSS, Mailafia ya ce; a shirye yake ya ba da rayuwarsa ga kasarsa kamar yadda Nelson Mandela ya yi, wato tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu. 

Sai dai a tattaunawar da ya yi da BBC Hausa, Mailafia ya ce bayanan da ya yin a cewa wani gwamna ne daga arewa shugaban Boko Haram, ya samu bayanan ne a ‘kasuwa’, kuma bai san zatukan na shi zai yadu haka ba. Inda ya tabbatar da cewa shi ba shi da wata hujja gamsasshiya.


Post a Comment

0 Comments