Wata Jaridar Amurka Za Ta Yi Taron Cusawa ‘Yan Nijeriya Kishin Kasa

 

Daga Muhammad Farouk

Wata Jaridar Amurka mai suna Global Patriot Newspapers (GPNews), ta shirya tsaf domin gudanar da wani taro na duniya bisa manufar dawo da kishin kasa ga ‘yan Nijeriya. 

GPNews za ta shirya wannan taron ne ta hanyar Intanet tare hadin guiwar kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna kasashe waje (NIDO) reshen jihar New Jersey dake Amurka, tare da taimakon ofishin Jakadancin Nijeriya dake birnin New York. 

Taron za a gudanar da shi ne a ranar 6 ga watan Maris, inda za a tattauna akan lamuran da suka shafi ci gaban kasa, kundin tsarin mulki, shugabanci, harkokin siyasa, tsaro, hakkin bil’adama, da kuma bangaren shari’a a Nijeriya, kamar yadda masu shirya taron suka tabbatar. 

A wata sanarwa, Mawallafi kuma Babban Editan GPNews, Simon Ibe da kuma shugaban kungiyar NIDO dake New Jersey, Dr Kazeem Bello, sun bayyana cewa; taron zai samu halartar kusoshin gwamnati, fitattun masana, masu rajin kare dimokuradiyya, manyan ‘yan gwagwarmaya da fafutikar kare hakkin bil’adama. 

“taron za a shirya shi ne a wani mataki na gano dalilan da ya sanya wasu ‘yan Nijeriya ba su kishin kasar da kuma bankado hanyoyin da zai magance wannan matsalar ta rashin kishin kasa. Sannan za a tattauna akan me yasa ‘yan Nijeriya ba sa alfahari da kasar su, ba sa muradin siyan abubuwan da ake sarrafawa a kasar, sannan kullum cikin tsinewa kasar suke yi”, inji sanarwar. 

Sanarwar ta ci gaba da cewa; taron zai maida hankali wajen fahimtar da ‘yan Nijeriya muhimmancin son kasar su da kuma karfafawa gwamnati wajen bunkasa alakar dake tsakanin ‘yan Nijeriya a daidaiku da kuma tsarin shugabanci. 

A cewar sanarwar, taken taron zai kasance ‘mu so Nijeriya da farko’, ‘Mu yi kishin kasarmu’, ‘mu rika siyan kayayyakin da ake sarrafawa a kasarmu’, ‘mu bunkasa Nijeriya’, ‘mu bada rayukanmu ga Nijeriya’. 

Masu shirya taron sun ce bayanan yadda za a halarci taron ta Intanet wanda za a fara shi da misalin karfe hudu na yamma za a sanar daga baya. 


Post a Comment

0 Comments