Yabon Sahabin Manzon Allah Sayyidina Ali Ya Jawowa ‘Yar Wasan Hausa Aisha Izzar So Suka


Daga Muhammad Farouk

MADOGARA ta labarto cewa; Matashiyar ‘yar wasan Hausa Fim na Kannywood wato Aisha Abdurrauf wacce aka fi sani da Aisha Izzar So ta sha zagi da suka da la’anta daga masu bibiyarta sakamakon amfani da shafinta da ta yi na Instagram a ranar Alhamis din 25 ga watan Fabarairu da ta yi ta taya daukacin al’ummar Musulmi murna da ranar zagayowar ranar haihuwar Sahabin Annabi (S) wato Sayyidina Ali Bn Abu Dalib. 

Hakan da ta yi bai yi wa wadansu daga cikin mabiyanta dadi ba, inda aka samu wadanda suka rika bin ta da zagi da suka da yarfe da nuna cewa ‘yan shi’a kadai ke murna da ranar haihuwar Sayyidina Ali, lamarin da wadansu kuma suka jinjinata mata da bata kariya tare da kalubalantar masu zaginta. 

Sai dai sukan da wadansu mabiyan na ta suka yi mata ya bai wa ‘yar wasan Hausan mamaki da takaici, inda ta yi wani bidiyo na martani da yammacin ranar Juma’a 26 ga watan Fabarairun 2021 ta kuma wallafa a shafinta na Instagram. Bidiyon mai tsawon minti uku da dakika biyu wanda wakilin MADOGARA ya kalla bidiyon, Aisha Abdurrauf a bidiyon ta kasance cikin yanayi na damuwa da takaici da mamaki, inda ta ce: “Assalamu alaikum, ina ma kowa fatan barka da yamma, ina yi wa kowa fatan alheri”, inji ta. 

Aisha Izzar So ta ci gaba da cewa: “jiya na yi ‘posting’ din bidiyo ina cewa ina taya daukacin al’ummar Musulmai zagayowar Haihuwar Sayyidina Ali (AS). To wasu suna ta maganganu suna ta tambayata wai ni ‘yar shi’a ce? Wasu kuma suna tsine min, wadansu kuma suna zagina, wasu suna la’anta ta, wadansu kuma ga su nan dai. To kuma duk na ji dai, kuma duk nagode. Da wadanda ma duk suka taya daukacin al’ummar Musulmai murna”, ta tabbatar. 

Aisha Izzar so ta jefo wata tambaya inda ta ce; “dama sai dan shi’a kadai yake son Sayyidina Ali? Dan shi’a ne kadai yake son Sayyidina Ali? Cab!” ta tambaya cikin yanayi na damuwa da fushi. 

Aisha Izzar so har wala yau a cikin bidiyon ta ci gaba da cewa: “dan uwan Manzon Allah (SAW), kuma surukin Manzon Allah, Sahabin Manzon Allah, yau na yi ‘posting’ saboda na taya daukacin al’ummar Musulmi zagayowar ranar haihuwarsa, wasu suke zagina, suke tsine min, suke la’anta ta, to wani katon ko katuwar gardin kuke so na je na taya murna ko waye? Kuna ‘nice’ kuna waye da waye? Shi kuke so?” ta tambaya cikin yanayi na damuwa. 

Aisha Izzar So ta kara da cewa: “wanda suke zagina nagode. Zamu hadu a can. Wallahi kun bani mamaki! Akwai wadanda suke cewa za su yi ‘unfollowing’ dina saboda kawai na taya al’ummar Musulmai zagayowar haihuwar Sayyidina Ali, dan uwan Manzon Allah (SAW), tsatsonsa, kofar ilimin Manzon Allah (SAW). Saboda na taya daukacin al’ummar Musulmi wasu suke tsine min, wasu suke zagina, to duk nagode. ‘Yan shi’a kadai suke son Sayyidina Ali,” ta karkare. 

Ita dai Aisha Abdurrauf ta shahara ne a shirin nan mai dogoron zango da ake kira IZZAR SO. Wacce ta fito a mai jan ragamar fim din a bangaren mata, a yayin da Lawal Ahmad ya kasance mai jan ragamar fim din a bangaren maza. 


Post a Comment

0 Comments