Yadda ‘Yan Bindiga Suka Dira A Makaranta Suka Sace Dalibai Mata A Jihar Zamfara

Daga Muhammad Farouk 

Wadansu ‘yan bindiga sun yi sace daliban makarantar Sakandaren gwamnati dake Jangebe a karamar Hukumar Talatan Mafara a jihar Zamfara. 

Karanta labarin nan; YANZU-YANZU: 'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata A Zamfara

MADOGARA ta labarto cewa; lamarin ya auku ne da safen ranar Juma’a. 

Majiyarmu ta Jaridar Daily Trust ta labarto wani mazaunin kauen Kawaye mai suna Sadi Kawaye ya shaida cewa; ‘ya’yansa biyu masu suna Mansura da Sakina suna daga cikin wadanda aka sace. 

 “a halin yanzu ina kan hanyar zuwa Jangebe kan wannan lamari mai firgicin gaske da ya auku. An shaida min cewa sun afka wa makarantar da misalin karfe 1 na dare ne”, inji shi. 

Da majiyarmu ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce ba zai yi magana a kai ba. 

“ku bani karin lokaci. Ba zan iya cewa wani abu ba a yanzu,” ya tabbatar. 

Sace dalibai matan na zuwa ne kasa da makonni biyu da wadansu ‘yan bindiga suka sace dalibai a makarantar kimiyya ta gwamnati dake Kagara a jihar Neja. 

Karanta labarin nan; ‘Har Yanzu Ba A Tantance Adadin Daliban Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A GSC Kagara Ta Jihar Neja Ba’

Maharan har wala yau sun afka a dakin kwanan dalibai da na Malamai, inda suka kwashe su suka yi daji da su. 

Duk da shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaro da su tabbata sun kwato su, sai dai har yanzu daliban na hannun ‘yan bindigar. 

A ranar Alhamis ne, gwamnan jihar ta Neja, Sani Bello ya yi zargin cewa gwamnatin Tarayya ta yi watsi da su kan lamarin kwato daliban Kagara din. 

A wani sakon murya da ya yi yawo a shafukan sada zumunta, wani mutum da ya yi magana a madadin masu garkuwa da jama’ar ya yi barazanar za su bar daliban da yunwa har sai sun mutu. 

Wannan shi ne karon farko a Nijeriya da ‘yan bindiga suka samu kwarin guiwar sace dalibai a makarantu daban-daban a kasa da makonni biyu.

Sace dalibai na farko da aka yi a Nijeriya ya auku ne a ranar 14 ga watan Afrilun 2014, inda ‘yan Boko Haram suka dira a makarantar Sakandaren gwamnati ta mata dake garin Chibok suka yi awon gaba da dalibai fiye da 300. 

Shekaru hudu bayan sace daliban, wadansu ‘yan bindigar suka dira a makarantar kimiyya ta gwamnati dake Dapchi a jihar Yobe, inda suka sace dalibai 119. 

A cikin watan Disambar 2020, an sace dalibai maza fiye da 300 a makarantar kimiyya ta gwamnati dake garin Kankara a jihar Katsina. 


Post a Comment

0 Comments