Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Mutum 23 A Wani Sabon Hari A Kaduna

 Daga Muhammad Farouk

Aruwan ya ce gwamnatinsu ta samu rahoto daga hukumomin tsaro cewa ‘yan bindiga sun kai hari a wadansu kauyuka dake jihar Kaduna, ciki harda garuruwan dake da makwabtaka da jihar.

A ranar Talata ‘yan bindiga suka kashe mutum 23 a wani sabon hari da suka kai a kananan hukumomi biyar a jihar Kaduna.

Mummunan harin na ‘yan bindigar sun kai shi ne a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da kuma Kauru.

Samuel Aruwan, Kwamishinan lura da tsaron cikin gida, shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

MADOGARA ta labarto Aruwan na cewa wadannan hare-hare na ‘yan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ashirin da uku.

“sakamakon yanayin matsalar tsaro da ya faru a jihar a cikin awa 24, gwamnatin jihar Kaduna ta samu rahoto daga hukumomin tsaro yadda aka kashe mutum 23 a hare-hare mabambanta a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, da Kauru,”, inji shi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; “A karamar hukumar Birnin Gwari an kashe mutum 10 a harin da aka kai a Ungwan Gajere da Kutemeshi. Wadanda aka kashe sun hada da; Abdu Hasan, Sufyanu Musa, Faisal Zubairu, Abdullahi Hasan, Ali Abdu, Rabiu Aliyu, Zubairu Yau, Bukar Yusuf, Mamman Ibrahim da kuma Dankande Musa”.

Ya ce kuma wadanda suka samu rauni sun  hada Baushi Alu, Rabe Sani, da kuma Usama Sani.

“A karamar hukumar Igabi kuma, ‘yan bindigar sun kashe wani mai suna Dayyabu Yahuza a tsakanin kauyukan Sarkin Baka da Dankyawai dake kusa da Gidan Kurmi,” inji Kwamishinan.

“A karamar hukumar Giwa kuma,  ‘yan bindigar sun kai hari a kauyen Janbaba inda suka kashe wani mai suna Yakubu Sule”, ya tabbatar.

Ya ci gaba da cewa; “A kauyen Kishisho dake karamar hukuma Kauru wadansu ‘yan bindiga da ake zargin sun fito ne daga jihar makwabta sun kashe: Danlami Sunday, Abbas Abou, Sati Yakubu, Shaba John, da John Francis”, inji shi.

Ya kara da cewa; “A karamar hukumar Chikun kuwa, ‘yan bindigar sun kashe mutum biyar a kauyen Gwagwada-Kasaya dake gundumar Kunai. Wadanda aka kashe sun hada da Habila Ibrahim, Samaila Audu, John Musa, Birnin Aboki, da Ali Aboki.

“Haka zalika a kauyen Agwa a karamar hukumar Chikun an kashe wani mai suna Bitrus Joseph a sabon harin da aka kai. Duk a Chikun din, ‘yan bindigar sun kashe wani a kusa da Bugai a lokacin da mutanen kauyen suka dakile harin ‘yan bindigar”, ya tabbatar.

Gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya nuna damuwarsa bisa wadannan kashe-kashe kamar yadda sanarwar ta tabbatar, inda ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan da suka rasa ‘yan’uwansu.

Post a Comment

0 Comments