Yajin Aikin 'Yan A-Daidaita-Sahu Na Ci Gaba Da Gurgunta Harkokin Sufuri A Kano


An shiga rana ta biyu ta yajin aikin da direbobin babura masu kafa uku da aka fi sani da adaidaita sahu suke yi a jihar Kano.

Shugabannin kungiyar sun ce sun tsunduma yajin aikin ne saboda ƙin amincewa da matakin hukumar sa ido kan zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA) na sanya musu harajin naira 100 a kullum.

Wakilin BBC HAUSA da ke jihar Kano ya ruwaito cewa a safiyar Talata ma an ci gaba da yajin aikin yayin da hanyoyi suka kasance fayau a kwaryar birnin.

Sai dai ya kara da cewa wasu kungiyoyi da dai-daikun masu hali sun dauki gabarar taimakawa dalibai da ƙananan 'yan kasuwa wajen kai su wuraren huldarsu.

Wasu rahotanni ma sun ce gwamnatin jihar ta samar da wasu motocin safa-safa da za a yi amfani da su wajen harkokin sufuri domin maye gurbin baburan masu kafa uku.

Baburan masu kafa uku su ne al'ummar jihar musammam marasa karfi suka fi amfani da su wajen gudanar da zirga-zirgarsu ta yau da kullum.Post a Comment

0 Comments