Kashe 'Yan Sanda A Garin Aba Ya Jefa Garin Cikin Rudani


Daga Muhammad Farouk

Makonni biyu da kai hari ofishin ‘yan sanda dake Omoba a karamar hukumar Isiala-Ngwa South dake jihar Abiya, a yau Talata wadansu ‘yan bindiga sun kone ofishin ‘yan sanda na World Bank Housing Estate dake Abayi a garin Aba. 

Jaridar Daily Trust ta labarto cewa ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda guda biyu masu mukamin ASP da kuma Kofur a harin  da suka kai. 

Rahotanni sun tabbatar da cewa da misalin karfe 2:30 na Asubahin ranar Talata suka dira a ofishin ‘yan sandan, inda bayan sun kaddamar da hare-hare suka kuma tsere da makamai daga ofishin ‘yan sandan. 

Wata majiya daga ‘yan sanda wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana majiyarmu cewa; lamarin ya haifar da rudani da rashin kwanciyar hankali a garin, inda ‘yan sanda yanzu ke aiki cikin tsoro a yankin. 

Tuni ‘yan sanda suka takaita zirga-zirga a ta wurin ofishin ‘yan sandan da aka kona, wanda hakan ke kara sanya firgici da damuwa a wurin. 

Majiyarmu da ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna, bai dauki wayar ba inda daga bisani ma ya kashe wayar. 


Post a Comment

0 Comments