'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 35 A Sabon Harin Da Suka Kai Jihar Zamfara

 

Daga Muhammad Farouk 

Rahotannin dake shigo mana na nuni da cewa ‘yan bindiga sun kari hari a kauyen Sabuwar Tunga dake karkashin mulkin Dankurmi a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda suka kashe mutum 35.

Majiyarmu ta SaharaReporters ta labarto cewa; lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis, inda ‘yan bindiga suka dira a kauyen a Babura suka yi kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba a kauyen. 

Wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa; harin ya auku ne a daren ranar Alhamis, inda ya ce ko da ganin yadda maharan suka kai harin, tsara shi suka yi kafin su kai shi. Ya kuma tabbatar da cewa; bayan sun dira a kauyen sun kashe mutane, har wala yau kuma sun kwashe dabbobin mutanen kauyen suka yi dazuka da su. 

“mun gano gawarwaki 35 bayan harin, kuma da yawa daga cikin mutanen kauyen har yanzu ba a gansu ba. Sun zo ne cikin tsakar dare, suka bude wuta kan mutanen kauyen, suka fara harbin kan mai uwa da wabi, sannan suka kona gidajen mutane”, ya tabbatar. 

Ba yau ‘yan bindiga suka fara kai hare-hare a Zamfara ba, sun dai suna kaddamar da hare-haren. Inda ‘yan bindiga suka barnata noma da kiwo a jihar, tare da kashe-kashen mutane da sace su suna biyan kudin fansa musamman mazauna kauyuka. 

A ranar Juma’a ma, ‘yan bindiga sun sace dalibai makata fiye da 300 a makarantar gwamnati (GGSS) dake Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da su. 

Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 1 na dare, inda suka kwashe dalibai matan a motocin bas. 

Wani mazaunin kauyen Kawaye mai suna Saidu Muhammadu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yarsa Mansura da Sakina suna daga cikin wadanda aka sace. 


Post a Comment

0 Comments