'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 46 Cikin Awa 48 A Arewacin Nijeriya

 

'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 46 a arewacin Nijeriya cikinawa 48 bayan wasu hare-hare guda uku.

Mutum 10 ne Boko Haram ta kashe bayan wani makami da ta harba cikin birnin Maiduguri ranar Talata, inda mutum 47 suka jikkata, a cewar gwamnatin Jihar Borno.

Cikin waɗanda Boko Haram ta jikkata har da ƙananan yaran da ba su kai shekara 10 ba.

Kamfanin dilancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa 'yan bindiga sun kashe mutum 18 ranar Laraba a harin da suka kai wasu ƙauyuka na Jihar Kaduna.

Kazalika, an kashe wasu 18 a harin da aka kai jihar Katsina tare da ƙona gidaje.

'Yan fashin daji na kashe ɗaruruwan mutane yayin hare-haren babu gaira babu dalili a jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna da Sokoto da Neja.


-Rahoton BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments