Hukumomin tsaro a Kaduna sun tabbatar da mutuwar
mutum biyu sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Akwando dake
karamar hukumar Kachia a jihar, inda suka kashe wani Dattijo mai suna Dikko
Bagudu.
A sanarwar da kwamishinan lura da harkokin tsaron
cikin gida ya fitar, Samuel Aruwan, ya ce ‘yan bindigar sun tare titin Sabon
Birni zuwa Rikau dake karamar hukumar Igabi inda suka kashe wani mutum mai suna
Ibrahim Abdulmumin, wanda yake mazaunin kauyen Rikau ne. Inda kuma suka raunata
wani mutum mai suna Sahabi Shafiu, wanda yake da ne ga Sarkin kauyen na Rikau.
Rahotanni sun ce wadanda lamarin ya shafa suna kan
hanyar dawowa ne daga kasuwar mako-mako dake ci a Sabon Birni, inda ‘yan bindigar
suka tare su a hanya.
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna damuwarsa
bisa wannan lamarin, inda ya mika ta’aziyyah ga iyalan wadanda lamarin ya
shafa. Tare da yin addu’ar samun lafiya ga wanda aka raunata.
0 Comments