'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Banga Tara A Jihar Neja

Daga Wakilinmu

'Yan bindiga sun kai hari  a jiya Talata da rana a kauyen Kuchi dake karamar Hukumar Munya dake Jihar Neja. Amma daga baya suka zarce zuwa cikin karamar hukumar Kachiya dake Jihar  Kaduna dake makwabtaka da karamar Hukumar Munya din kamar yadda wakilinmu ya tabbatar mana. 

'Yan bindigar dai sun yi ba-ta-kashi da 'yan Banga tare da Mutanen wannan yankin. Inda aka samu asarar rayukan wasu samarin dake yankin lokacin wannan ba-ta-kashin. Sannan 'yan bindiga sun kashe 'yan banga guda tara. 

Har yanzu dai ba a kammala tantance adadin wadanda 'yan bindigar suka sace ba. 

Haka nan a shekaranjiya Litinin da daddare, wadannan 'yan bindiga sun kashe Dagacin Gidigori dake karamar hukumar Rafi a Neja. Sannan sun kashe wani dalibi a makarantar Government Science College Kagara a  jiya Talata da daddare. 

Post a Comment

0 Comments