‘Yan Sanda Sun Cafke Babban Jam’in Hisbah Dake Kama Karuwai Da Matar Aure A Otel A Kano

 

Daga Muhammad Farouk 

Hukumar Hisbah ta Kano ta tabbatar da labarin da ake yadawa cewa jami’an ‘yan sandan yankin Nomansland sun kama babban jami’inta mai suna Sani Nasidi Uba Remo, wanda ake zargin ‘yan sandan sun kama shi ne a wani Otel dake Sabon Gari tare da matar aure.

Shi dai Sani Remo ya kasance OC a Hisbah wanda ke lura da kama Karuwai kafin a maishe shi bangaren kama masu barace-barace a jihar kamar yadda majiyarmu ta Sahelian Times ta labarto.

Majiyarmu ta labarto mana cewa; jami’an ‘yan sandan ‘Nomansland Police Division’ ne suka kama shi, inda suka ce sun kama Sani Nasidi Uba Remo ne bayan da suka samu korafi daga mijin matar. Inda suka tabbatar da cewa sun kama shi ne a dakin Otel dake Sabon Gari tare da matar.

Mataimakin Kwamandan Hisbah ya je ofishin ‘yan sandan domin karbar belinsa, inda ‘yan sandan suka hana bayar da belinsa da farko, amma bayan doguwar tattaunawa, ‘yan sandan sun mayar da lamarin Hedikwatar Hisbah din domin gudanar da kwakkwaran bincike.

A martanin da Babban Kwamandan Hisbah na Kano Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina, ya mayar, ya ce tabbas sun samu wannan labarin mai girgizawa. Inda ya kara da cewa; tuni ya kafa kwamitin bincike domin bankado mene ne ya faru dangane da wannan zargin da ake yi wa babban jami’insu. Wanda ya yi alkawarin bayar da rahoto nan da kwana uku kafin daukar mataki na gaba.

 


Post a Comment

0 Comments