‘Yan Shi’a Sun Yi Maulidin Sayyidina Ali A Zariya

Shaikh Abdulhamid Bello (a tsakiya)

Daga Wakilinmu 

‘Yan Harkar Musulunci a Nijeriya da aka fi sani da ‘yan shi’a almajiran Shaikh Ibraheem El-Zakzaky sun yi taron maulidin Sahabin Manzon Allah (S), Sayyidina Ali Dan Abu Dalib. 

Taron wanda ya gudana a makarantar Fudiyya dake Babban Dodo Zariya, ya samu halartar dimbin mabiya shi’ar daga sassa daban-daban na yankin Zariyar. Wakilinmu da ya halarci taron ya labarto mana cewa; an gudanar da taron ne da yammacin ranar Alhamis din 25 ga watan Fabarairun 2021.

Malam Aminu Sakatare wani Malamin Darikar Tijjaniyya shi ne wanda ya fara gabatar da jawabi a taron. Cikin jawabinsa ya karanto tarihi da falalar Sayyadi Ali, inda ya ce shi ne mutum na farko kuma na karshe da aka haifa a dakin Ka'aba. 

Malam Aminu Sakatare


Bayan ya kammala ne sai wani Malamin daga Darikar Tijjaniyya mai suna Malam Ibrahim Usman Na Malam Tijjani Khalifa Zaria ya gabatar da na shi jawabin, inda shima ya bada tarihi Sayyadi Ali, wanda ya ce an haife shi ne a ranar 13 ga watan Rajab, inda ya ce wata ruwayar kuma an haife shi a ranar 29 ga wata.

Ya cigaba da cewa daga cikin siffofin Imam Ali akwai sadaukarwa, tawadi’u, zuhudu, ilimi, basira, da zalakar harshe.

Malam Ibrahim Usman 


Shugaban ‘yan Shi’ar na Zariya, Shaikh Abdulhameed Bello ya yi ta’aliki kan jawaban da aka gabatar. Inda ya fara da godiya ga Allah. Sannan ya bayyana cewa; “khulasan maganganun da aka yi shi ne lallai Imam Ali (AS) babban baiwa ne ga wannan al'umma. Allah ta'ala ya yi masa baiwa. Allah ya bashi matsayi, Yana da daraja, yana da ɗaukaka. Darajojin nasa ma la tu'addu wala tuhsa, shiyasa ma ko da za a yi magana sai dai kowa ya ɗauki wani ɓangare ya tunatar. Wancan ma ya ɗauki wani ɓangare ya tunatar, ko kuma a dunƙule a ɗauki wasu janibobi ta yiwu mafi muhimmanci a cikin su a yi tsokaci akan su, ku san dukan su akan ɗauki kamar nasaba, abin da ya shafi tarihin haihuwa, makamantan wannan”, ya lurantar. 

Wani bangare na mahalarta taron


Ya ci gaba da cewa: “wasu kuma sun ɗauki abin da ya shafi darajoji, da abin da ya shafi falaloli na Amiril Mu'uminin (AS) musamman ma na jarumta da ilimi. To wannan zamanin da muke ciki, to alhamdulillah wannan lokaci ne na su Ahlul Baiti (AS)”, inji shi. 

Taron dai Dandalin Matasa na ‘yan shi’ar ne ya gudanar, inda a karshe aka yanka Alkaki sai takaitaccen jawabi daga shugaban Dandalin matasan na Zaria, Malam Isma'il D. Usman ya gabatar. 

Sannan suka bada kyautuka ga daya da na biyu da na uku bisa gasar wasan kwallon kafa da suka shirya a tsakanin matasa a Zariya. Wanda matasan Cocin CTC dake Sabon Garin Zariya suka zo na daya, Harisawa suka zo na biyu a yayin  da Dandalin Matasan suka zo na uku. 
Post a Comment

0 Comments