YANZU-YANZU: An Bude Kasuwar Shasha Da Aka Yi Rikici Tsakanin Yarbawa Da Hausawa

Gwamna Seyi Makinde Na Jihar Oyo
  

*Za A Fara Rabon Tallafi Ga Wadanda Rikicin Ya Shafa 

A wani mataki na ganin zaman lafiya ya dawo a garin Shasha bayan rikicin da ya barke a tsakanin Yarbawa da Hausawa a kasuwar, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da safiyar ranar Talata, ya bayar da umurnin a sake bude kasuwar. 

Umurnin sake bude kasuwan ya biyo bayan zaman da aka yi a tsakanin shugabannin al’ummar garin na Shasa wanda ya gudana a dakin taro na Western Hall Sakatariyyar dake Ibadan. 


Post a Comment

0 Comments