Daga Muhammad Farouk
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa yara bakwai sun raunata sakamakon fashewar wani bom bisa tsautsayi da ya auku a karamar hukumar Igabi dake jihar.
“hukumomin tsaro sun bayar da rahoton fashewar
wani bom bisa tsautsayi da aka sanya a Unguwan Mangwaro dake karamar hukumar
Igabi,” kamar yadda sanarwa daga Kwamishinan lura da tsaron cikin gida, Samuel
Aruwan ya tabbatar.
“rahoton ya bayyana
cewa wadansu yara ne suke wasa a yankin inda suka dauko abin fashewar da aka
binne a wata gona a kusa da su, inda suka rika wasa da abin ba tare da sun san
ko mene ne ba. A yayin wasan ne, bom din ya fashe bisa tsautsayi a kusa da gidansu”,
inji Aruwan.
“dukkanin yaran bakwai sun samu rauni
sakamakon fashewar bom din, inda yanzu haka suke asibitin koyarwar na Jami’ar
Ahmadu Bello dake Shika”, ya tabbatar.
Da yake bayyana
damuwarsa, gwamna Nasir El-Rufai ya ce lamarin ya zo da sauki, tunda yaran da
suka raunata suna karbar magani yanzu haka.
Ya nemi hukumomin tsaro
da su yi bincike kan lamarin, sannan ya shawarci al’umma da su zama masu sanya
ido kan dukkanin abin da suka gani ba su gane masa ba a ko’ina ne.
An sanar da hukumomin
tsaron kan lamarin domin ganin sun gudanar da bincike domin dakile aukuwar
hakan a gaba.
An kuma nemi al’ummar
jihar Kaduna da su tuntubi dakin tsaron jihar Kaduna domin bayyana musu duk
wani bayani kan wani abin fashewa da suka tsinta a fadin jihar ta hanyar
wadannan lambobi 09034000060 da 08170189999.
0 Comments