YANZU-YANZU: Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Su Burutai, Sadiq A Matsayin Jakadun Nijeriya

 

Daga Muhammad Farouk 

Rahotannin dake shigowa MADOGARA na nuni da cewa; a yau Talata majalisar Dattawan Nijeriya sun tabbatar da mukaman da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaron Nijeriya a matsayin Jakadun Nijeriya a kasashen waje. 

Sabbin Jakadun da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sunayensu gaban majalisar Dattawan sune; Janar Abayomi Olonisakin (mai ritaya) daga Ekiti, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya) daga Borno, Vice Admiral Ibok- Ette Ibas (mai ritaya) daga Kuros Ribas, sai Air Vice Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya) daga Bauchi, da kuma Air Vice Marshal Muhammad S. Usman (mai ritaya) daga Kano.

Tabbatar da su ya biyo bayan rahoton kwamitin Majalisar Dattawan kan hulda da kasashen waje wanda Sanata Adamu Bulkachuwa ke yiwa jagoranci. 

Yunkurin da shugaban Majalisar mara rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi na ankarar da Majalisar akan korafin da aka shigar kan dakatar da tabbatar da su, nan take shugaban majalisar Dattawan Ahmad Lawan ya tsayar da Sanatan kan tado da wannan korafin. 

Abaribe ya nemi Bulkachuwa ya yi bayanin me yasa korafin da aka shiga akan su aka yi watsi da shi, amma sai Sanata Lawan ya ce korafin ba shi da kwakkwaran hujja. 


Post a Comment

0 Comments