Yanzu-Yanzu: ‘Yan Sanda Sun Cafke Macaroni A Zanga-zangar Shege Ka Fasa A Legas

Jami’an tsaron ‘yan sandan Nijeriya sun cafke Debo Macaroni a ranar Asabar a zanga-zangar shege ka fasa da suka fito a daidai kofar Lekki Toll Gate a yau Asabar a garin Legas duk da gargadin da gwamnatin tarayya ta yi wa masu zanga-zangar. 

Tuni masu zanga-zangar suka shirya gudanar da zanga-zangar a yau domin nemawa wadanda aka kashe a zanga-zangar EndSars adalci tare da kuma Allah-wadai da yunkurin bude Toll Gate din na Lekki da gwamnatin Legas ke yunkurin yi. 

Macaroni wanda ya kasance shahararren dan wasan barkwanci a garin Legas, ‘yan sandan sun kama shi ne a yayin da yake daukar bidiyon zanga-zanga da wayarsa. Inda aka yada kama shi da aka yi kai tsaye a shafin Instagram da safiyar yau Asabar. 

A cikin bidiyon an jiyo shi yana cewa an kai shi ofishin ‘yan sanda, inda ya nemi da ‘yan Nijeriya su kwantar da hankalinsu. 

“dan sanda abokin ku ne,” aka jiyo shi yana cewa kafin a kwace wayarsa. 

Ya zuwa hada wannan rahoton, akalla mutum 13 wadanda suka fara bayyana domin gudanar da zanga-zangar ‘yan sandan suka kama da misalin karfe 8 na safe. 

Gwamantin Buhari tuni dama ta gargadi masu gudanar da zanga-zangar, inda suka ce akwai hukuncin mai tsanani ga duk wanda ya shiga cikin masu zanga-zangar da nufin tarwatsa zaman lafiyar al’umma. Inda su kuma masu shirya zanga-zangar suka ce wannan barazanar ta gwamnatin tarayya ba zai hana su fitowa ba. 

Post a Comment

0 Comments