Yau Asabar Daya Ga Watan Rajab -Fadar Sarkin Musulmi

 

Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar na III

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar na III ta ce ranar Asabar ce 1 ga watan Rajab, shekarar 1442 bayan hijirar Annabi SAW daga Makkah zuwa Madina.

Sakataren kwamitin ganin wata a fadar Sarkin Musulmi, Alh. Yahaya Muhammad Boyi ya shaida wa BBC cewa a ranar Juma’a aka ga watan na Rajab wanda kuma Asabar ta kasance 1 daga watan.

Hakan na nufin saura mako takwas watan azumi na Ramadan ya kama bayan watan Sha’aban.


Post a Comment

0 Comments