Zaben Jamhuriyar Nijar: Bazoum Mohamed Na Dab Da Zama Zababben Shugaban Ƙasar


Daga BBC Hausa

Sakamakon zaɓen Jamhuriyar Nijar zagaye na biyu ya nuna cewa Bazoum Mohamed na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki na dab da lashe shi.

Alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta CENI ta fitar ya zuwa yanzu sun nuna cewa Bazoum ne yake da sama da kuri'a miliyan 2 da dubu 500.

Dan takarar jam'iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane ya samu kuri'a sama da miliyan 1 da dubu 800.

Wakiliyar BBC da ke Niamey Tchima Illa Issoufou ta ce hukumar zaben ta CENI ta wallafa sakamakon gundumomi 259 daga cikin 266.

Sai dai mataimakin shugaban hukumar CENI Dr Aladoua Amada ya ce duk da yake saura sakamakon gundumomi 7 amma ba za su iya canja akalar sakamakon ba kasancewar a zagayen farko na zaben shugaban kasa dan takara Bazoum ne ya lashe zaben.

Ta ce da misalin karfe 11 na safiyar Talata ne ake sa ran sanar da sakamakon wucingadi na zaben.

A ranar Lahadi aka gudanar da zaben zagaye na biyu inda aka fafata tsakanin Mohammed Bazoum da abokin karawarsa Mahamane Ousmane.

Bazoum dai ya samu goyon bayan ƴan takarar da suka zo na uku da na hudu a zagayen farko na zaben, shi kuma Ousmane ya samu goyon baya daga gamayyar jam'iyyun hamayya 18.

A zagayen farko na zaben dan takara Mohamed Bazoum na jam'iyya mai mulki ya samu kashi 39.3 yayin da tsohon shugaba Mahamane Ousmane yake da kashi 16.9 cikin ɗari.

Bangaren hamayyar ya yi tur da zargin magudin zaɓe sannan ya ce ba zai yadda da sakamakon zagaye na biyu ba matuƙar ya lura an tafka magudi.

Kungiyoyin da suka sa ido kan yadda zaben ke gudana a kasar sun ce duk da cewa akwai 'yan kura-kurai da aka tafka, amma an samu ci gaba a bangaren shirye-shiryen yadda zaben ya gudana da kuma yanayin fitowar jama'a wajen kada kuri'a.

'Yan takarar shugabancin kasa talatin ne suka fafata da juna a zagayen farko na zaben da aka gudanar a watan karshen watan Disambar 2020 don karbar ragamar mulki daga hannun Shugaba Mahamadou Issoufou, bayan karewar wa'adin mulkinsa na biyu na tsawon shekara goma.

Zaben shi ne irinsa na farko da wani zababben shugaban kasa zai mika mulki cikin ruwan sanyi ga wani takwaransa da za a zaba.

Sai dai kuma masu sharhi kan al'amuran yau da kullum a kasar na cewa, ko ma wane ne zai zama sabon shugaban kasar a Jamhuriyar Nijar, zai fuskanci kalubala daban-daban da suka hada da tabarbarewar tsaro da cin hanci da rashawa da kuma talauci.Post a Comment

0 Comments