Zanga-zangar Shege Ka Fasa: An Girke Jami'an Tsaro a Lekki Toll Gate

 

An girke Jami'an tsaro a Lekki Toll Gate

An girke jami’an tsaro a toll gate din unguwar Lekki da ke Legas yayin da wasu rahotanni ke cewa ƴan sanda sun kama masu zanga-zangar fiye da 13 da misalin karfe takwas na safe.

An ga hotunan ƴan sandan ɗauke da makamai a toll gate din na unguwar Lekki bayan sake buɗe hanyar ta Lekki kamar yadda BBC Hausa suka labarto

Tuni wasu ƴan Najeriya ke kiran ƙaddamar da zanga-zanga a Lekki toll gate inda jami’an tsaro suka buɗe wa masu zanga-zanga wuta a watan Oktoban 2020.

Wasu ƴan ƙasar na son ƙaddamar da zanga-zanga ta adawa da sake buɗe Lekki toll gate suna masu cewa sai an tabbatar da adalci ga waɗanda suke zargin jami’an tsaro sun harba.

Post a Comment

0 Comments