Zulum Ya Yi Wa Likita Bayarabe Kyautar Kusan Naira Miliyan 14

 

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wani likita Bayarabe kyautar mota da kuma kuɗi kusan naira miliyan 14.

Sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar ta ce gwamna Zulum ya karrama likitan ɗan asalin jihar Ogun ne saboda jajircewarsa duk da rikicin Boko Haram amma bai tsere ba daga aikinsa a babban asibitin Monguno kamar yadda BBC ta labarto.


An yi wa likitan kyautar sabuwar mota


Duk da hare-haren Boko Haram amma Dakta Isa Akinbode ya ci gaba da kula da marar lafiya a Monguno a tsawon shekarun da aka shafe cikin rikicin Boko Haram, a cewar gwamnatin Borno.

“Bayan ya yi ritaya, likitan duk da rahotanni sun ce an taɓa sace shi kafin Boko Haram ta sake shi a Monguno amma ya ci gaba da bayar da taimako a asibiti.”

Sannan gwamnatin Borno ta kuma ba ƴarsa aiki a jami’ar Maiduguri.

Gwamnatin ta ce an tattara masa kuɗaɗensa na ladar aikinsa ne inda kuma yanzu za a ci gaba da biyansa duk wata ƙarƙashin wata yarjejeniyar aikin wuccin gadi da ya ƙulla da gwamnatin Kashim Shettima.

Post a Comment

0 Comments