Abubuwa Goma Sha Daya Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabon Mai Tangale

Malam Danladi Sanusi Maiyamba 

Daga Muhammad Farouk 


Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya a ranar Laraba ya ayyana Malam Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sabon Mai Tangale na 16. 

Ayyana shi ya biyo bayan kwashe kwanaki 52 bayan rasuwar Dr Abdu Buba Maisheru II, Mai Tangale na 15. 

Ga abubuwa goma sha daya da ya kamata ku sani dangane da sabin Mai Tangale: 

1. An haifi  Malam Danladi Sanusi Maiyamba  a ranar 12 ga watan Fabarairun 1966 a karamar hukumar Billiri dake jihar Gombe.

2.Ya yi karatun Firamarensa a ‘Billiri Primary School’ inda ya samu satifiket din Firamarensa a shekarar 1979.

3.Ya halarci makarantar Sakandare ta ‘Government Day Secondary School, Army Barrack’ dake Yola daga 1979 zuwa 1984. 

4. Sannan ya je makarantar kimiyya da fasaha ta ‘Federal Polytechnic’ dake Bauchi ya karanci satifiket a sha’anin mulki. 

5. Tsohon dalibin ‘Administrative Staff College of Nigeria (ASCON),’ dake Legas ne, inda ya samu shaidar kammala makarantar a bangaren gudanar da tattalin al’umma a 2013. 

6. Sabon Mai Tangale ya kwashe akalla shekaru 34 yana aikin gwamnati a bangarori daban-daban da ya hada da ma’aikatu da hukumomi da sashe-sashe na gwamnati. 

7. Ya yi aiki a ma’aikatar ili a jihohin Bauchi da Gombe a tsakanin shekarar 1987 da 1996.

8. A lokacin da aka samar da jihar Gombe daga Bauchi a 1996, ya koma Gombe inda ya yi aiki da ma’aikatar bada tallafi na jihar Gombe daga 1996  zuwa 2004, sannan ya koma ma’aikatar lafiya daga 2004 zuwa 2005.

9. An maida shi kotun daukaka kara na Shari’a na Gombe ya yi aiki daga 2005 zuwa 2011. Sannan ya koma Hukumar lura da kananan hukumomi daga 2011 zuwa 2016

10. A tsakanin 2016 zuwa 2021 ya yi aiki a ma’aikar lura da dabbobi da kiwo daga 2016 zuwa 2018 da kuma hukumar majalisar jihar Gombe daga 2018 zuwa 2021.

11. Maiyamba yana da aure da ‘ya’ya.


Post a Comment

0 Comments