Akwai ‘Yan Bindiga Dubu 30 A Jihar Zamfara –Sarakunan Zamfara

 


Daga Muhammad Farouk 

Sarakunan jihar Zamfara sun tabbatar da cewa akwai ‘yan bindiga fiye da dubu Talatin a fadin dazukan jihar. Sarakunan gargajiya na jihar sun shaida wa shugabannin hafsoshin tsaro hakan ne a yayin da suka kai ziyara a jihar.

A wani labarin kuma, shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan bindigar jihar Zamfara wata biyu da su mika wuya, kamar yadda gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle ya tabbatar a wani jawabi da ya gabatar a gidan Talabijin na jihar a ranar Talata. 

Matawalle ya ce shugaban kasar har wala yau ya bada umurnin aika sojoji dubu shida jihar domin murkushe ‘yan bindigar idan sun gaza mika wuya. 

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne awanni kadan da Sarakunan gargajiya na jihar suka shaida wa shugabannin hafsoshin tsaro wadanda suka kai ziyara a jihar, inda suka ce akwai ‘yan bindiga fiye da dubu 30 a dazukan Zamfara. Adadin da suka ce ya zarce adadin rundunar sojin dubu 10 da aka kai jihar domin su kawo karshen rashin tsaron da yake addabar jihar. 

Umurnin na shugaba Buhari ya zo ne mako daya da hana tashin jirage tashi a fadin jihar, tare da haramta ayyukan tatsar ma’adanai a jihar, inda shugaban kasar ya ce ana musayar wadannan ma’adanai ne da makamai a jihar. 

A jawabin gwamnan jihar, ya ce ya kai ziyarar kwanaki hudu a Abuja, inda ya yi wa shugaba 

Gwamnan ya bai wa Sarakunan gargajiyar da kuma shugabanni a jihar umurnin zama a inda suke domin sanya ido kan ayyukan mutane da kuma ayyukan da ba a yarda da su ba. 

“a don haka mun haramta daukar mutum sama da biyu a babur nan take. Mun haramta jerin gwanon Babura a lungu da sako na jihar, muna bai wa hukumomin tsaro umurnin da su cafke duk wadanda suka ga sun karya wannan dokar”, ya tabbatar.

A karshe gwamna Matawalle ya tabbatar da haramta ayyukan ‘Yan Sa Kai, inda ya ce duk wanda aka kama rike da bindiga kowacce iri ce za a yi maganinsa. 


Post a Comment

0 Comments