Allurar Rigakafin Korona Dubu 55,920 Ta Iso Jihar Zamfara

Kwamishina lafiya na Jihar Zamfara Hon. Muhammad Yahaya Kanoma na yiwa 'Yan jaridu bayani zuwan Allurar a Gusau


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau


 Yanzu haka gwamnatin jihar Zamfara ta karbi allurai rigakafin Korona dubu 55, 920, watau COVID 19 daga gwamnatin Tarayya.

Jagoran amso allurar rigakafin, kwamishinan lafiya na jihar zamfara, Alhaji Yahaya Muhammed Kanoma, ya bayyana cewa, gwamnati zata tsaya tsayin daka  domin taga kowane dan jihar anyi masa wannan allurar rigakafin.

"Kwamishina Kanoma,ya  bayyana cewa,akaron farko mutane da  dama ne za su karbi alluran a jihar, kuma matakin allurar rigakafin ne tun daga  ‘yan shekaru 18 zuwa sama ne za a yi ma allurar a faddin jihar, inji Kwamishina.


Hon. Kanoma ya bayyana mutanen da za su fara karbar allurar rigakafin cutar za su kasance masu fada a jiya bayan an kammala yima gwamna Bello Matawalle Maradun da manyan mukarra ban gwamnati, daga nan sai ma’aikatan lafiya, sarakunan gargajiya, da masu sayar da man fetur ‘yan jarida da sauran su.

Kuma yanzu haka wasu likitocin suna karbar horo kan yadda za a ba da rigakafin da zarar an kammala horon za su fara aikinsu.

Kwamishinan ya yaba wa hukumomin UNICEF da WHO kan kokarin da suke yi na tabbatar da allurar rigakafin ta isa Jihar ta Zamfara.

Kuma mun yi kyakkyawan shiri don adana alluran ta hanyar tabbatar da wadatar ciyar wutar lantarki tare da kara xakunan sanyi masu awanni 24, tare da wutar lantarki da injunan samar da wutar lantarki guda biyu da kuma makamashin hasken rana.

Post a Comment

0 Comments