An Kama Soja Da Ake Zarginsa Da Ba 'Yan Ta'adda Kakin Soja Da Makamai A Zamfara


Daga Husaini Ibrahim, Gusau

An kama wani sojan kasa da ake zargi da bai wa 'yan ta'addan kakin soji da alburusai a jihar Zamfara.

 Mataimakin Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnati  jihar Zamfara, Alhaji Bashir Maru ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani ga wasu rahotanni da wasu kafafen yada labarai suka bayar na wasu mutane 60 da ‘yan bindiga suka sace a Gundumar Ruwan Tofa da ke cikin Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.


Alhaji Bashir ya ce gwamnatin jihar tana jiran rahotannin rundunar Sojin na binciken da ta yi dangane da lamarin.

"Kuma Ya yi kira ga 'yan jarida da kungiyoyin da kafofin yada labarai da su tabbatar da sahihancin labaran su koyaushe kafin su watsashi.

Ya sake nanata yadda gwamnatin jihar za ta hada gwiwa da kafafen  yada labarai a koyaushe don tabbatar da daidaito a rahotonsu kan al'amuran da ke bukatar tabbatar masu da gaskiya.

Bashir Maru ya ce mutanen Ruwan Tofa sun kashe ‘yan fashi da yawa don kare jama’arsu amma rahoton na kafafen yada labarai bai nuna hakan ba.

Ya kuma tabbatarwa ma ‘yan jaridu irin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na kasancewa da kowa a koda yaushe tare da sauke nauyin da ke kanta.

Duk kokarin da mukayi na jin ta bakin  Daraktan Hulda da Jama’a na Soja, Birgediya Janar Muhammad Yerima, amma abin yaci tura.

Post a Comment

0 Comments