An Sace Kiristoci Fiye Da 500 A Nijeriya Cikin Shekara Daya, Inji CAN


Bbc Hausa ta labarto cewa; kungiyar kiristocin Nijeriya, CAN sun koka, inda suka ce a shekarar da ta gabata kawai, an sace membobinsu fiye da 500.

Kungiyar reshen arewacin Nijeriya ne suka bayyana hakan. Babban Sakatare na kungiyar reshen arewacin Nijeriya, Rabaran Joseph Hyap ya ce kungiyar na da dukkan shaidar da ke nuni da wannan adadi na membobinta da aka sace su.

Rabaran Hyap ya ci gaba da cewa “ita da kanta gwamnatin jihar Kano ta ce an yi garkuwa da sama da mutum 2000 a shekarar da ta wuce, don haka idan muka ce an sace namu membobin sama da 500 ba mu yi karya ba”, ya lurantar.

Hyap ya yi nuni da cewa; ya tara Fastoci akalla 1, 500 wanda ya zauna da su domin tattara bayanan mutanen da aka sace da wadanda aka kasha, wanda ya ce ta wannan hanyar ne  suka gano wadanda lamarin ya rutsa da su, inda ya ce sun biya kudin fansa domin karbo wasu daga cikinsu, wasu kuma babu labarinsu har zuwa yau

“Ko a makon da ya wuce an sace wani fasto da sakatarensa da wasu mambobi, an sako uku daga ciki amma sauran har yau babu amo babu labari,” in ji Hya.

Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta fito ta karyata ikirarin kungiyar.

Post a Comment

0 Comments