AN SAKE KUNNOWA ABDULJABBAR WUTA: Kotu Ta Bayar Da Umurnin A Bincike Shi Bisa Zargin Barazanar Kisan Kai


Daga Muhammad Farouk

A wani abu mai kama da an sake kunnowa fitaccen Malamin nan, Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara wuta ne, wata kotun Majistare mai zama a Kano a ranar Juma’a ta umurci Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, da ya tabbata ya gudanar da bincike kan Shehin Malamin bisa zarginsa da ake yi yana bata suna da kuma barazanar kisa ga rayuwar wani. 

Mai Shari’a Mustapha Sa’ad-Datti na kotun, shi ne wanda ya bayar da umurnin sakamakon karar da lauyan Sheikh Abdallah Pakistan wato Abdulrahman Nasir ya shigar gaban kotun inda ya nemi da a hukunta Shaikh Abduljabbar din kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya labarto. 

Wadanda ake kara ya hada da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar, lamarin da ya sanya kotun ta bukaci Kwamishinan 'yan sandan ya yi bincike. 

Umurnin mai dauke da lamba KA/CMC14/003/2021 ta jadadda cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar akwai bukatar ya kammala bincikensa ya kuma mika ga kotun kafin 27 ga watan Maris.

Post a Comment

0 Comments