An Sanya Dokar Hana Fita A Jangebe Dake Jihar Zamfara


Daga Muhammad Farouk
 
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar hana fita a garin Jangebe dake karamar Hukumar Talata Mafara dake jihar Zamfara daga ranar Larabar 3 ga watan Maris. 

Majiyarmu ta labarto mana cewa; dokar ta biyo bayan hatsaniyar da aka samu ne a garin na Jangebe bayan dawo da dalibai mata da aka 'yanto daga hannun 'yan bindiga, wanda har ta kaima sojoji suka yi harbe-harbe suka harbi wasu mutanen garin. 

Majiyarmu ta shaidawa MADOGARA cewa; mutanen garin ba su ji dadin yadda gwamnatin jihar ta yi da batun sace dalibai matan ba, tun daga lokacin da aka sace su har zuwa dawowa da su da aka yi. 

Kwamishinan yada labarai na jihar, Sulaimanu Tanau Anka a wata sanarwa da ya fita a ranar Laraba ya ce gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin dakile aukuwar rashin zaman lafiya a garin. 

Ya kuma kara da cewa; "akwai gamsassun hujjoji da suke nuni da cewa ayyukan wata kasuwa a garin yana taimakawa 'yan bindigar a garin da ma makwabta. A don haka, dukkanin hada-hadar kasuwanni an dakatar da su har zuwa wani lokaci da za a sanar", ya tabbatar. 

Ya ci gaba da cewa; "nauyi ne a wuyan gwamnatin jihar ta kare dukiya da rayukan al'umma ta dukkan yadda za ta iya", ya lurantar. 

A karshe ya nemi jami'an 'yan sandan jihar da su tabbata dokar ta yi aiki a garin. 

Post a Comment

0 Comments