An Yi Yunkurin Juyin Mulki A Jamhuriyyar NijerDaga Muhammad Farouk

Sojojin sun yi wani yunkuri na juyin mulkin da bai yi Nasara ba a Jimhuriyar Nijar a ranar Talata da misalin karte uku na Asuba. 

Nijar dai ta auka cikin hayaniyar siyasa ne tun bayan da aka tabbatar da Bazöum Mohammed a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a zagaye na biyu.

Lamarin da bai yi wa babban jagoran 'yan Adawa na kasar ba, Mahammane Ousmane inda ya ja da sakamakon zaben da ya baiwa Bazöum Mohamed nasara.

A ranar Juma'a mai zuwa ne ake sa ran za a yi bikin rantsar da sabon zababben shugaban kasar, wanda shi ne karon farko da za ai bikin mika mulki daga Gwamnatin farar hula zuwa farar hula.

Shugaban kasar Mai barin Gado Mouhammadou Issoufou ya shafe kimanin shekaru goma yana jan ragamar kasar a matsayin zababben shugaban kasa na farar hula.

Post a Comment

0 Comments