Ana Fama Da Matsanancin Rashin Ruwa A Zariya


Daga Wakilinmu 

Kamar kowacce shekara musamman a lokacin da ba damina ba, sanannan abu ne cewa a garin Zariya dake jihar Kaduna ana fama da matsanancin wuyar ruwa ta yadda lamarin ya kai ana fita dibar ruwa maza da mata tunda asubar fari. 

Jama'a da dama na fitar neman rijiyoyin da suke da ruwa inda suke musu kawanya domin dibar ruwan. 

Ba rijiyoyi kadai ba, harma da burtsatsai mutane na zuwa su bi layi tare da tarin kayan diban ruwan su domin ganin sun samu ruwan da za su kai gidajensu. 

Hoton dake kasa wanda wakilinmu ya aiko mana ya labarto mana cewa; wurina dibar ruwa ne guda Uku a Anguwar Jushi dake cikin garin Zariya, inda ko wanne da jama'a suna zaman jiran layi ya zo kansu su diba. 

Duk da yake gwamnatin jihar Kaduna a karkashin gwamna Nasiru El-Rufai ta jawo ruwan famfo a Anguwar kamar yadda gwamnatin ta yi a sauran Unguwanni, sai dai famfunan sun zama kamar hoto don kuwa sai a yi wata cur ba tare da an kawo ruwa ba kamar yadda wakilinmu ya labarto mana. Wanda hakan ke haifar da matsanancin wuyar ruwan a garin. 

Post a Comment

0 Comments