BA YA TA HAIHU: 'Muhammadu Sanusi Ba Shi Ne Khalifan Tijjaniyyah Ba'

 


Dariqar Tijjaniya ta musanta baiwa tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II shugabancinta na Nijeriya.


Sheikh Mahi Nyass, shugaban darikar Tijjaniya na duniya wanda ake kira da Khalifatum Arrm, ya bayyana hakan yayin da yayi jawabi ga manema labarai a Sokoto.


Jaridar The Punch ta wallafa cewa, Nyass, wanda shine da kuma magajin Shehu Ibrahim Nyass, yace in har za a yi nadi ana tantancewa sannan a zaba daga cikin mabiyanta na Najeriya da Senegal.


Irin wadannan hukunci ana tattaunawa ne sannan a amince kafin a sanar. Bayan an zaba mutum, akwai wasikar amincewa daga malamai wacce Khalifatul Arrm zai saka hannu kuma ya mika ga wanda aka nada,” Nyass yace.


Ya ce Sanusi bai nuna bukatar kujerar ba kuma shugabannin basu riga sun fitar da tsarin da za a bi ba wurin wannan nadin.


“Hadin kan ‘yan kungiya yana da amfani kuma ina kira ga kungiyar da ta mayar da hankali wurin bauta, kara dankon zumunci da kaunar juna,” yace.


Sheikh Ibrahim Dahiru-Bauchi, da ga fitaccen malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kwatanta labarin nadin Sanusi da labarin bogi.

Post a Comment

0 Comments