Babu Sulhu Tsakaninmu Da Saudiyya -Mayakan Houthi

Wata sanarwa daga Gwamnatin Saudiya ta fitar na nuni da cewa sulhun mai  muhimmanci ne ga ilahirin kasar wanda ta ce zai kasance karkashin jagorancin  Majalisar Dinkin Duniya.

Ministan waje na Saudiya Yerima Faisal bin Farhan ya fadawa taron manema labarai a Riyadh cewa bukatarsu ita ce a kawo karshen amfani da bindigogi a wannan yaki.

A yanzu haka mayakan Houthi dake Yemen sun hau kujeran naki game da wannan ta yi daga kasar Saudiya. 

Sai dai wadansu masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin Saudiyyar ta nemi wannan sulhun ne ganin yadda Mayakan Houthin ke ruwan wuta a wuraren da ke da alaka da tattalin arzikin Saudiyyar, wanda hakan ke Barazana ga tattalin arzikin na Saudiyya. 

Post a Comment

0 Comments