Babu Tabbas Cewa Sojin Nijeriya Sun Kashe Masu Zanga-zanga A Lekki Ta Jihar Legas, Inji Amurka

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana a cikin rahotan ta na shekara-shekara cewar babu tabbacin bayanai dangane da kisan da ake zargi sojojin Nijeriyar sun aikata a bara.

Rahotan ya ce babu sahihanci kan mutanen da aka ce sojojin sun harbe lokacin da suka tarwatsa masu zanga-zanga akan hanyar Lekkin.

Kungiyar Amnesty International ta ce mutane 10 suka mutu lokacin harbin, amma gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da rahotan kungiyar kuma babu wata kungiya ta daban da ta tabbatar da yawan mutanen, sai dai gwamnati ta ce mutane 2 sun mutu sakamakon lamarin.

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewar sojoji sun je wurin da makamai, abin da ya sa aka kafa kwamitin bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.

Post a Comment

0 Comments