Bayan Kammala Bayar da Shaidu Kotu Ta Dage Shari'ar Shaikh Zakzaky Zuwa Watan Mayu


Wata babbar kotun jihar Kaduna ta sake dage zaman sauraron shari’ar jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky har zuwa ranar 25 na watan Mayun bana.

A dazu-dazun nan ne kotun da ke sauraren karar ta Sheikh Ibraheem Zakzaky ta dage zaman shari’ar har zuwa ranar 25 ga watan Mayu na wannan shekarar ta 2021. 

Wannan na zuwa ne bayan gabatar da manyan shaidu kimanin goma sha biyar da masu shigar da kara na bangaren gwamnatin Kaduna suka gabatar kan kisan kiyashin da sojoji suka yi a garin Zariya a shekaru shida da suka gabata.

A na su bangaren lauyoyin da ke kare El-Zakzaky,  sun nunar da cewa dukkanin shaidun da aka gabatar ba su tanadi kwararan hujjoji masu karfi da shari’a za ta iya amfani da su ba, balle har su yi tunanin kare kansu. Sun ce suna cike da fatan za a wanke jagoran na su daga duka zarge-zargen tayar da zaune tsaye da suka yi sanadiyar rayukan mutum sama da dari uku.

Shaikh Zakzaky ya sha musanta zarge-zargen a yayin da magoya bayansa ke ci gaba da gudanar da muzaharorin ganin an sake shi a Abuja, Kaduna da Zariya. 

Post a Comment

0 Comments