Binciken Wadanda Suke Rayuwar Da Ta Fi Karfinsu Ya Zama Doka A Nijeriya

 
     Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC

Daga Muhammad Farouk

Mataimakiya ga shugaban kasar Nijeriya kan kafofin sada zumunta, Laurette Onochie, ta ce hukumomin da ke yakar cin hanci da rashawa wato EFCC da ICPC za su binciki 'yan Nijeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsu musamman a shafukan sada zumunta.

Ms Onochie ta shaida hakan ne a shafinta na Twitter a ranar Litinin, inda ta ce za a gayyaci irin wadannan mutanen domin a bincike su kan yadda suka mallaki kadarori da arzikin da suke shakatawa da su.

Onochie ta ce, "binciken yadda mutum ya ke rayuwarsa za ta kasance dole a Nijeriya bisa bin sharudda na doka".

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa a makon da ya gabata ya fitar da sanarwa cewa wajibi ne duk wani ma'aikacin banki ya bayyana kadarorin da ya mallaka.

Post a Comment

0 Comments