Cikakken Bayanin Mahamane Ousmane Kan Kalubalantar Zaben Shugaban Kasa Na Jamhuriyyar Nijer

Dan takarar jam'iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane
 

Daga Zaharaddeen Abbas 

A makon da ya gabata ne aka bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Jamhuriyyar Nijer, inda Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar ta ce Bazoum Mohamed na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki ne ya lashe zagaye na biyu na zaben da aka gudanar a ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI ta fitar dazun nan sun nuna cewa Bazoum ya samu sama da kuri'a miliyan 2 da dubu 501.

Dan takarar jam'iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane, wanda yake biye masa, ya samu kuri'a sama da miliyan 1 da dubu 968.

Bazoum ya samu kashi 55.75 na kuri'un da aka kada, yayin da Mahamane Ousmane, wanda tsohon shugaban kasar ne, ya samu kashi on 44.25.

Bangaren hamayya ya ya yi tur da zaben, inda ya ce an tafka magudi, sannan ya ce ba zai yadda da sakamakon zagaye na biyu ba matuƙar ya lura an tafka magudi.

Mahamane Ousmane ya fara ne da cewa a hirarsa da DW Hausa, inda ya ce: “sakamakon da ita kungiyar zabe ta bada, ta bada shi bisa abubuwan da suke zuwa mata. Kowanne dan takara shima doka ta ba shi damar na daya; ya samu wakili a kowanne rumfar zabe. Na biyu; wakilinsa ya kawo mishi sakamakon zaben da ya fito daga wannan rumfar zabe. Na uku kuma ya yi lissafi, ya yi kididdiga bisa abin da ya samu bisa sauran abokan takararshi suka samu”. 

Ya ci gaba da cewa: “To, alhamdulillahi sakamakon da muka samu, sai mu yi wa Allah godiya, mu kara yi wa kasa godiya, wanda wakilanmu suka kawo mana, ya bamu cewa ni ne na ci zabe. A cikin kasha 100 na samu kasha 50.30. Shi abokin takarata a cikin 100 ya samu kasha 49.07”, ya tabbatar. 

Sannan ya kara da cewa: “Alhamdulillahi, ina kara maimaitawa jama’a kasar wannan godiyata da wannan goyon baya da suka ba ni bi da bi. A takaice abin da zance shi ne; lallai mun gano an yi aringizo da yawa, musamman ma wajen yankuna na arewacin jihohinmu. Arewacin Tahoa. Akwai kuma inda aka yi aringizo da yawa, wanda ta wuce iyaka”, ya lurantar. 

Ya karkare da cewa: “Sakamakon zaben nan mun yi watsi da shi, saboda wannan ne muka kai wannan kararraki, tare da hujjoji. To ai wajibi ne mu kai kara, tare da hujjoji”. 


Post a Comment

0 Comments