CIN KUDIN MAKAMAI: Ana Cacar Baki Tsakanin Garba Shehu Da Monguno

 


Daga Muhammad Farouk

An fara cacar baka tsakanin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu bisa cin kudin makamai da ake zargin tsoffin shugabannin hafsoshin tsaron Nijeriya da ya hada da Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, Janar Abayomi Olonisakin da babban hafsan sojin sojan ruwa Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; da babban hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar sun yi, inda Malam Garba Shehu ya ce ba zai yiwu a ce wadannan kudade sun bace ba ko an cinye su a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Idan ba ku manta ba. mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ya ce har yanzu ba a san yadda aka yi da makudan kudaden da shugaba Buhari ya bayar don sayen makamai da sauran kayan aiki don yaki da matsallolin tsaro da suka addabi kasar ba.

A hirarsa da BBC Monguno ya bayyana cewa gwamnati na bakin kokarinta wajen shawo kan matsalar tsaron da ake ci gaba da fuskanta, da wasu 'yan Najeiya ke ganin gwamnati ba da gaske ta ke yi ba domin tana ta jan kafa game da al'amarin.

''Babu wanda ya san abin da aka yi da wadannan kudaden, amma da yardar Allah shugaban kasa zai bincika domin a gano inda aka kai su ko kuma a ina kayan suka shiga,'' in ji Monguno.

Kungiyar gwamnoni ma in ji jami'in tsaron sun fara magana a kan cewa "an bayar da kudade ta ko ina amma babu abin da aka yi da su, saboda haka na tabbatar shugaban kasa tun da ba mai wasa da hakkin al'umma bane, zai taimaka."

Munguno ya jaddada cewa ''Tun da dai ba a yi wani binciken kwarai ba, ba zan ce wani abu ba, amma dai kudi dai tabbas sun salwanta, kayan dai ba a gani ba, kuma sabbin shugabannin tsaro sun ce su fa ba su ga kayyakin tsaro da ake magana ba a kai.''

Ƙila wasu suna kan hanya daga Amurka, daga Ingila ko daga wasu wurare, amma yanzu a kasa ban gani ba su ma ba su gai ba,'' in ji shi.

Sai dai Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu a ranar Juma’a ya ce ba zai yiwu a ci kudin makamai ba a karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari. Garba Shehu ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin da yake hira da gidan Talabijin na Channels kan batar dabon da ake zargin Dala Biliyan Daya sun yi wadanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ware domin a siya makamai da su don yaki da ta’addanci a Nijeriya.

Garba Shehu ya ce dala biliyan daya da shugaba Muhammadu Buhari ya fitar a 2018 saboda siyan makaman, lallai an yi amfani da su yadda ya dace.

Sai dai Garba Shehu ya ci gaba da cewa; “ina mamakin yadda kake magana akan Dala biliyan dayan da aka cire daga asusun man fetur ta kasa bisa yarjewar gwamnonin jihohi, kuma aka yi amfani da su wajen siyan makamai ga soji. Ina mai tabbatar maka da cewa ba abin da ya sami kudin nan. Hujjar da ake bayarwa da maganar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA Mongunu a hirar da ya yi da BBC Hausa, da alama an murguda zancen ne ko ba a fahimce shi ba”, ya lurantar.

Garba Shehu ya ci gaba da cewa: “NSA ya yi bayani biyu masu muhimmanci. Na daya; bamu da gamsasshen bayani, wanda hakan magana ce ta gaskiya. Na biyu; makaman da aka siya har yanzu ba duka aka kawo ba”, ya tabbatar.

Ya kara da cewa; “a cikin watan Agustan 2018, aka bar gwamnatin Nijeriya ta siya jiragen yakin Super Tucano Aircraft guda 12 domin fuskantar yakin da muke yi a arewa maso gabashin Nijeriya. Kari kan hakan, an siyo wadansu makaman na soji. Sashen sojin ruwa, kusan kashi 100 na makamansu an kawo musu”, ya tabbatar.

Ya lurantar da cewa suma bangaren sojin sama an kawo musu jiragen helikwafta na kai hare-hare. Inda aka siyo 35 daga Ukraine. “wadansu daga ciki an kaddamar da su kai tsaye a gidan talabijin na kasa. Mun siyo jiragen ‘drones’, amma bangaren soji, akwai matsalolin da aka fuskanta wajen siyo na su makaman. Makaman ya rika zuwa daya bayan daya”, inji shi.

Ya tabbatar da cewa sun siyo manyan makamai daga Daular Larabawa, UAE, inda ya ce yanzu haka ana tattaunawa ta diflomasiyya tsakanin Nijeriya da UAE. “ministan tsaron Nijeirya ya gana da Jakadan UAE a Nijeriya, domin tattauna yadda za a kawo su Nijeriya ba tare da wata matsala ba”, ya tabbatar.

Garba Shehu ya wanke NSA, inda ya ce mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ba yana magana kan an cinye kudin makamai ba, saboda ba a ma ci kudaden makaman ba. Inda ya ce; “na saurari hirar da aka yi da shi a rediyo. Na kuma fahimce shi sosai. Babu inda ya yi zargin an cinye kudin makaman. Ba a kawo makaman ba, tabbas wannan gaskiya ne ba a kawo ba. Ba abu ne da ake siyansa a shago ba, sai ka nema sannan za a kawo maka”, inji shi.

Ya karkare da cewa; “ministar kudi ce ya kamata ta zo da bayanai kan hakan. Ina fatan a ‘yan kwanakin nan ta zo da shi. Mutane suna son su siyasantar da lamarin ne. Suna son nuna cewa babu bambanci tsakanin gwamnatin APC da PDP. Tabbas ba daya suke ba. Sace kudin makamai ba zai taba faruwa a gwamnatin Buhari ba”, inji shi.  

 

Post a Comment

0 Comments