Da Ina Da Dama Da Na Karrama Shaikh Zakzaky A Matsayin Jagoran Zaman Lafiya A Kasarnan, Inji Marubuciya Rahma Abdulmajid

Daga Muhammad Farouk

Fitacciyar marubuciyarnan, Malama Rahama Abdulmajid ta jinjinawa Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky a daidai lokacin da ake bukin cikarsa shekaru 70 a duniya a lissafin Hijiriyyah, inda ta ce da tana da damar ba shi 'award', da za ta bashi a bangaren jagoran zaman lafiya a Nijeriya baki daya. 

Rahma Abdulmajid ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook, a wani rubutu da ta yi me taken; 'SHEKARARSA 70 A DUNIYA', inda ta wallafa bayanai kamar haka; 

A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai.

1. Shekara shida kenan da aka daure shi daga shi har matarsa 

2. A cikin wannan shekarunsa Saba'in Gwamnatoci suka karar da 'ya'yansa.

3. A cikin wannan shekarun an kashe dubban mabiyansa maza da mata manya da yara har da na goye da suke asalin yan Najeriya masu hakkin tsaro da kare lafiya a wuyan gwamnati.

4. A cikin wadannan shekarun aka rushe duk wani waje da ya mallaka. 

5. A cikin wannan shekarun ne Kotu ta rika bayar da belinsa gwamnati na take umarnin kotu.

6. A cikin wannan shekarun duka bai kira mabiyansa da su dauki makami kamar yadda inyamurai ke dauka su kwana lafiya, yarbawa ke dauka su kwana lafiya, Fulani ke dauka su kwana lafiya. 

7. Laifinsa daya shi ne ya zabi hanyar da ya ke ganin ita ce addininsa a kasar da kundin tsarin mulkinta  yace kowa na da 'yancin yin addini yadda yake so cikin walwala.

DA INA DA DAMAR BAYAR DA AWARD HAKIKA ZAN BAIWA SHEKH ZAKZAKY AWARD DIN JAGORAN ZAMAN LAFIYA A KASAR NAN. 

ALLAH YA KUBUTAR DA KAI YA BAKA LAFIYA, YA SAKA MAKA

Post a Comment

0 Comments