Dalilanmu Na Janyewa Daga Mukabala Da Abduljabbar - Jama’atu Nasril Islam

 

Daga Muhammad Farouk 

Jama’atu Nasril Islam (JNI) a karkashin shugabancin mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, ta janye daga sanya ido a mukabalar da za a yi da Shaikh Abduljabbar, Malamin Darikar Kadiriyya da kuma Malaman Kano daga bangarorin Izala da Darikar Tijjaniyyah bisa wadansu zarge-zarge da ake yi wa Shehin Malamin. 

Karanta labarin nan; An Saka Ranar Muƙabala Tsakanin Sheikh Abduljabbar Da Malaman Kano

Takardar wanda Sakataren kungiyar, Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya sanyawa hannu a ranar 3 ga watan Maris din 2021, ya tabbatar da cewa su a matsayinsu na kungiya ba za su taba shiga mukabalar ba. 

JNI ta ce tana mai sake jaddada Allah-wadai dinta bisa; “kalaman batancin da Abdul-Jabbar na Kano ya yi ga fiyayyen halitta Muhammad (SWA), iyalinsa da kuma Sahabbansa, Allah ya yarda da su. JNI ba za ta taba yarda da wannan mukabalar ba”, suka tabbatar.  

JNI sun ce tunda fari kan hatsaniyar sun jinjinawa gwamnatin Kano bisa matakin da ta dauka na dakatar da aukuwar “tsinuwa a kasa tare da dakatar da ballewar rashin doka da oda. Mun yi tunanin gwamnatin za ta ci gaba da tuntuba a gaba kan wannan matsalar da ba iya jihar Kano kawai ta shafa ba, lamari ne da ya shafi kasa da ma duniya baki daya ga dukkanin wani musulmi na kwarai”, inji JNI din. 

Karanta labarin nan; Mun Goyi Bayan Shirya Mukabala Da Shaikh Abduljabbar –Kungiyar CIPEP

JNI ta ci gaba da cewa; “ta bayyana cewa matsalar an fantsama ta, gwamnati da wadansu daidaikun mutane sun sanya lamarin ya yi suna, inda suka daukaka (Abduljabbar) daga kalaman batancin da ya yiwa halittar da Allah ya fi so, Muhammad (SAW). Abduljabbar bai cancanci irin suna da daukakar da maida hankali da aka yi akan shi tun bayan faruwar lamarin”, inji su. 

JNI ta kara da cewa a maimakon mukabala da Abduljabbar wanda ya yi ‘batanci ga Manzon Allah (SAW)’, akwai shakku a imaninsa na Musulunci, a don haka babu bukatar sake ba shi wata dama domin sake bayyana “munanan kalamansa ga duniya”, suka lurantar. 

JNI sun ce da a ce gwamnatin Kano ta tuntubi wadanda ya kamata su tuntuba musamman wadanda aka gayyata domin su halarci mukabalar, da yanzu ba maganar mukabala ake yi ba. “a don haka, JNI tana tabbatar da cewa ba za ta halarci mukabalar ba, hakazalika babu wani reshenta da zai halarta”. 

A karshe sun yi wa gwamnatin Kano da Malaman da za a yi mukabalar da su fatan alheri, da kuma addu’ar Allah ya taimaka musu a dukkanin ayyukansu. “muna kuma fatan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da suke cikin lamarin za su sauya matsayarsu”, suka karkare. 

Karanta labarin nan; Lauyoyin Shaikh Abduljabbar Sun Janye Karar Da Suka Shigar Da Gwamnatin Ganduje

Sai dai wakilinmu ya mana labarto cewa; tuni al’umma a shafukan sada zumunta suka fara caccakar JNI din, inda suka ce; tabbas kungiyar yanzu ta tashi a matsayin uwar Musulmai, ta koma kare muradun wasu, inda wasu ma suka zarge ta da kare muradun hukumomin Saudiyya tare da daukar bangare a lamarin da ake zargin Malamin wanda ya fito ya karyata dukkanin zarge-zargen, harma ya kara da cewa shi kokari yake na kore karairayin da aka jinginawa Manzon Allah (SAW) da ya ce suna cikin “littafan Bukhari da Muslim”, ya tabbatar. 

Al'umma da dama na son a bai wa Shaikh Abduljabbar damar kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa, tunda ya fito ya karyata ya kuma yi zargin cewa an yanyanke masa jawabansa. 

Post a Comment

1 Comments

  1. Inda ba kasa kawai bukatarmu a bashi dama muji daga bakinsa

    ReplyDelete