Dan Uwan Shugaba Buhari Ya Gina Katafaren Gida A Abuja


Dan uwan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma dan Majalisar Tarayya, Fatuhu Muhammed, ya bayyana sabon gidansa da ya gina a birnin Tarayya Abuja. 

Muhammed, wanda yake dan majalisa ne mai wakiltar Daura/Maiadua/Sandamu a karkashin jam'iyyar APC, ya ce ya gina gidan ne "cikin shekara hudu". 

Dan Majalisar ya sanya hoton katafaren gidan a shafinsa na  Facebook, inda ya nemi 'yan'uwa da abokan arziki da su taya shi da addu'a bisa wannan nasarar da ya samu. 

“Alhamdulillah na kammala ginin gidana a Gwarinpa (Abuja) wanda ya dauke ni shekaru hudu kafin na kammala. Amma nagodewa Allah, ina bukatar addu'arku. Zan sanar da ku ranar da zan koma gidan insha Allah", ya wallafa a shafinsa na Facebook. 

Sai dai daga bisani, dan Majalisar ya goge rubutun na shi. 

                    Fatuhu Muhammad

A cikin watan Satumbar bara ne, dan Majalisar Fatuhu Muhammed ya yi barazanar kai wa wani mai amfani da shafin Facebook Mai suna Abdulbasi Maiadua hari saboda caccakarshi da yake yi. 

Dan Majalisar ya yi barazanar ne a cikin muryarsa da aka nada a yayin wata kiran waya, inda ya ce; "ina so ka nadi muryarnan. Ina mai gargadinka da ka sake tsokanata ka gani, ni ba sa'anka bane. Ba kuma sa'an maigidanka bane, idan ba ka fita sabgata ba, zan yi maganinka. Ka kai kara ta wurin duk wanda ka so a Katsina da ma Nijeriya", inji Fatuhu. 

Post a Comment

0 Comments