Duk Abin Da Ya Same Ni Ganduje Ne, Inji Jaafar Jaafar


Mawallafin Jaridun Daily Nigerian da kuma Daily Nigerian Hausa, Jaafar Jaafar ya bayyana cewar duk abinda ya same shi to Gwamnan jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje shi ne yake da alhakin abin. Jaafar, ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya rubutawa Sifeton 'yan sanda na kasa IG Adamu.

A ranar Juma'a da ta gabata, a wata tattaunawa da yayi da gidan Radiyo na BBC Hausa, Geamnan jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya karyata bidiyon dollar da jaridar Daily Nigerian ta wallafa, inda Gwamnan yace, wadan da suka saki wannan faifan bidiyon zasu dandana kudarsu nan ba da jimawa ba.

A saboda haka ne, Jaafar Jaafar ya rubuta wasika zuwa ga Sifeton'yan sanda na kasa IG Adamu, inda ya bayyana cewar rayuwarsa da ta iyalansa tana cikin hadari a sakamakon wannan furuci da Gwamnan yayi. 

Idan ba a manta ba a shekarar 2018 wannan jarida ta wallafa wasu hotunan bidiyo da aka hasko Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje yana karbar kudade a dalar Amurka, wanda dukkan shaidu suka nuna cewar daga hannun 'yan kwangila aka karbi wadannan kudade a matsayin ladangabe.

Kamar yadda Lauyansa Jaafar Jaafar, Barisat Abdullahi Gumel ya bayyana, Gwamnan Kano tare da magoya bayansa na yunkurin farwa Jaafar din don illata shi, a don haka, suke son ankarar da sifeton'yan sanda na kasa kan wannaj batu, a cewar Lauyan Jaafar Jaafar.

Post a Comment

0 Comments