Duk Wanda Kuka Gani Da Bindigar AK-47 Ku Dambara Mai Harsashi –Buhari Ga Jami’an Tsaro

 

Daga Muhammad Farouk

Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa jami’an tsaron kasar umurnin cewa duk wanda suka gani da manyan makamai wanda ya hada da bindigar AK-47, sun harbe shi.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakinsa, Malam Garba Shehu a wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, inda ya kara da cewa shugaba Buhari har wala yau ya kuma bayar da umurnin a afkawa ‘yan bindigar da suka ki su mika wuya.

Umurnin Shugaba Buharin na zuwa ne bayan da gwamnonin arewa maso gabashin kasar, suka bayyana shirinsu na samar da hadin guiwar hukumar tsaro da za ta yi yaki da ta’addanci a yankinsu. Sannan sun kuma nemi da a sauya salon yadda sojoji ke yaki da ta’addanci a yankin.

Idan za ku iya tunawa, shugaba Buhari ya hana tashin jiragen sama da kuma ayyukan arzikin kasa a jihar Zamfara a wani mataki na taimakon gwamnatin jihar wajen yaki da matsalar tsaro da ya addabi jihar.

Sai dai jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana adawarta da wannan matakin na hana tashin jirage a jihar ta Zamfara, inda suka yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta APC na  yunkurin ayyanawa jihar dokar ta baci.

A na shi bangaren, Gwamna Bello Matawalle, ya ce ya amince da umurnin na shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya bayyana hakan ne a hirarsa da gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba a shirinsu na ‘Politics Today’, inda ya ce dama jihar ba su da filin tashin jirage.

“na amince da umurnin shugaban kasa kan hana jirage tashi. Na amince na kuma yarda. Mutane ba su san cewa jihar Zamfara ba ta ma da filin jirgin sama ba. A don haka sauran jihohin da suke da filin tashin jirage suke kuma fuskantar irin wannan matsalar, me ye faru das u?” gwamnan ya tambaya.

 

Post a Comment

0 Comments