FUDMA Ta Sanya Wa Asibitin Jami'ar Sunan Farfesa Adamu Gwarzo

 


Daga Muhammad Farouk 

Jami’ar gwamnatin Tarayya dake Dutsin-Ma a jihar Katsina, FUDMA ta sanyawa asibiti sunan Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda yake shi ne wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN’ dake jamhuriyyar Nijer.

Shugaban Jami’ar FUDMA, Farfesa Armayau Hamisu Bichi shi ne ya bayyana hakan a yayin da yake bude asibitin a muhallin Jami’ar na dindindin dake Dutsinma a ranar Litinin. Farfesa Armayau ya ce an sanya sunan Farfesa Gwarzo ne biyo bayan amincewar hukumar gudanar da Jami’ar ta FUDMA.

A cewar Farfesa Armayau ya ce an yi wa Farfesa Gwarzo wannan karramar ne bisa lura da irin gudummawar da yake bai wa Jami’ar FUDMA.

Farfesa Armayau ya ci gaba da cewa; “idan aka cire gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina, babu wanda ya taimakawa jami’arnan kamar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo tun bayan kafa jami’arnan”, ya tabbtar.

Har wala yau Farfesa Armayau ya kara da cewa: “Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo matashi ne mai dattako da tsoron Allah wanda yake amfani da dukiyarsa wajen bunkasa bangaren zamantakewa da tattalin arzikin al’umma tare da taimakon wadanda ba su da karfi”, ya lurantar.

Farfesa Armayau Bichi ya jinjinawa shugaban Jami’ar ta MAAUN bisa gudummawa da taimakon da yake bai wa FUDMA, inda ya ce Jami’ar ta amfana matuka da irin gudummawar da ya ba su wanda ya hada da manyan motocin na miliyoyin naira domin amfanar daliban jami’ar. Ya kara da cewa; Farfesa Adamu Gwarzo har wala yau ya taimakawa jami’ar da kujeru, littafan UNESCO, da kuma motar daukar marasa lafiya domin amfanar asibitin Jami’ar.

A karshe ya yi addu’ar Allah ya kara daukaka Farfesa Adamu Gwarzo da iyalinsa, sannan Allah ya ba shi karfin guiwar ci gaba da taimakawa matasa ta hanyar ba su ingantaccen ilimi.

A na shi bayanin, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya mika godiyarsa ga Jami’ar FUDMA bisa sanya wa asibitin Jami’ar sunansa. Inda ya yi alkawarin ganin ya taimakawa Jami’ar ta FUDMA ta samu sahhalewar kasashen duniya domin hada kafada da kafada da Jami’o’in duniya. A cewarsa, duk jami’ar da kasashen duniya ba ta gamsu da ita ba, ana yi mata kallon jami’ar da ba ta zama ta duniya ba.

Sannan har wala yau ya yi alkawarin taimakawa jami’ar wajen ganin ta samu rijista da UNESCO, inda ya ce nan bada jimawa ba Jami’ar za ta zama ta biyu a kasarnan za ta kasance a karkashin UNESCO.

Ya karkare da cewa; dukkanin Malaman da ke sashen koyar da harshen Faransanci a jami’ar an ba su gurbin karatun digiri na uku wato PhD a Jami’ar MAAUN dake jamhuriyyar Nijer.

 

Ga wasu kadan daga cikin hotunan taron da aka yi; 


Post a Comment

0 Comments