GASAR ZAKARUN TURAI: An Bar Cristiano Ronaldo Da Dora Hannu A Ka


FC Porto ta yi waje da Juventus a gasar Champions League, duk da rashin nasara da ta yi da ci 3-2 a Italiya a wasan da suka yi ranar Talata.


Kungiyoyin sun buga wasa na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai don fayyace wadda za ta kai fafatawar quarter final.


Kungiyar ta Portugal ta ci wasan farko da suka yi a cikin Fabrairu da ci 2-1, yayin da Juventus ta ci 3-2, jumulla Porto ta kai zagayen gaba ne, bayan da ta ci kwallo biyu a Italiya.


Porto ta karasa fafatawar da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Mehdi Taremi jan kati a minti na bakwai da komawa zagaye na biyu.


Wannan ne karon farko da Porto ta kai Quarter finals a Champions League, bayan da ta ci wasan farko, tun bayan 2003-04 da ta yi nasara a kan Lyon.


A karo na biyar kenan ana cire Juventus a wasan zuwa daf da na kusa da na karshe a Champions League idan aka doke ta fafatawar farko.


Wanda Juventus ta yi bajinta a biyar din shi ne karawa da Atletico Madrid, inda tasha kashi da ci 2-0 a Spaniya, yayin da ta kai quarter finals a Italiya, bayan da ta ci 3-0 a 2018-19.

Post a Comment

0 Comments