Gwamna Matawalle Ya Ba 'Yan Ta'addan Zamfara Wa'adin Wata Biyu Su Yi Saranda

 

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara Hon Bello Muhammad Matawalle Maradun,ya ba "Yan ta'adan da suka addabi Jihar Zamfara wata biyu suyi Suranda da mika makaman su ko su gamu da fushin jami'an tsaro.

Matawalle Maradun ya bayyana haka ne alokacin da ya kabatar da jawabi ga al'ummar Jihar Zamfara a kan matsalar tsaro da da addabi Jihar.

Gwamna Matawalle ya fara da Waiwaye adan tafiya, Idan zaku iya tunawa, a ranar Jumma’a 26 ga watan Febreru shekara ta 2021 da misalin karfe dai na dare, wadannsu gungun ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suka afkama makarantar ‘yanmata dake Jangebe a Karamar Hukumar Talatar Mafara, a inda suka yi awon gaba da dalibai 279.

 Wannan abun bakin ciki ya girgiza al’ummar wannan Jiha da kasa da kuma duniya baki daya. Haka kuma, wannan ya nuna irin yanayin matsalolin tsaro da muke fama dasu a Jiharmu  dama wasu Jihohin da ke Arewacin Najeriya. Hakan ya kuma nuna irin tsananin bukatar da ake da ita na daukar kwararan matakai domin shawo kan wannan matsala baki daya.

"Matawalle ya kara da cewa,mun ceto wadannan daliabai 279 cikin koshin lafiya, kuma mun mika su ga iyalansu.

Nasara ceto Daliban ya sanya nayi tattaki zuwa Abuja domin ganawa da Shugaban Kasa da sauran masu ruwa da tsaki akan lamarin tsaro na kasa. Sakamakon wannan ganawa da muka yi, Mai Girma Shugaban Kasa ya aminta da turo karin sojoji dubu sittin zuwa Jihar Zamfara domin kara kaimi akan yaki da akeyi da ‘yan ta’adda a wannan jiha tamu.inji gwamna Matawalle.

 Haka kuma kamar yadda kuka sani, Shugaban Kasa ya bada umurni a kawar da duk wani da aka samu da bindigar Ak 47 ba tare da izini ba nan take.Kuma Majalisar Tsaro ta Kasa ta haramta shawagin jiragen sama a sararin jihar Zamfara tare da dakatar da aikace-aikacen hakar zinari a fadin Jihar Zamfar.a jawabin gwamna Matawalle.

"Ya kuma kara da cewa, Shugaban Kasa ya aminta da saka watanni biyu kacal ga dukkanin yanta’adda da su mika makamansu su rungumi zaman lafiya.Bugu da kari, kamar yadda kuka sani, tsarin da muka fito dashi na sulhu ya samar muna da abubuwa da dama wadanda suka hada da karbo makamai a hannun yanta’adda, kubutarda daruruwan wadanda aka yi garkuwa dasu, bude kasuwannin da aka rufe a baya da kuma raguwar hare-hare da kasha-kashe afadin Jahar nan.

"Duk da wannan kwarya-kwaryar zaman lafiyar da aka samu a wannan Jiha, akwai wasu bijirarru da suka ki su rungumi wannan tsari na zaman lafiya da Gwamnatita ta bullo dashi.

A kokarinmu na kawo karshen ta’addanci a Jihar Zamfara, Gwamnati ta yanke daukar wadannan matakai kamar Haka:
Duk bijirarrun da ke son shiga cikin tsarin sulhun zaman lafiya, dole ne suyi hakan nan da watanni biyu kacal;

Gwamnati na gargadin dukkanin ‘yan siyasa su guji dukkanin wadansu kalamai da ayukkan da zasu iya zama barazana ga zaman lafiya. Amba jamian tsaro umurni da su dauki matakin da ya dace akan duk wanda ya saba ma wannan umurni;

"An umurci dukkanin sarakunan gargajiya da shuwagabanin riko na Kananan Hukumomi da su kasance a yankunansu a kowane lokaci domin sa ido da tantance bakin da ke shige da fice a cikin yankunansu;

Kuma an haramta mutun fiye da biyu su hau babur daya a lokaci guda. Amba jamian tsaro umurni da su dauki matakin da ya dace ga duk wanda ya saba ma wannan doka;

Hakama an haramta gungun mashuna su yi tafiya tare a lokaci guda;

Gwannati ta damu kwarai da samun rahotannin ayukkan ‘yansakai, duk da dakatar da ayukkansu da aka yi. Don haka ina kara jaddada cewa haramcinnan yana nan daram.
Tuk da yake gwamanati ta na yabawa ayukkan ‘yanjaridu wurin yaki da ta’addaci a Jihar nan, ta kuma damu da irin yadda wadansu tsirarrun kafofin yada labarai, musamman ma na yanar gizo, ke yada labarum karya da batanci wanda ke sa jama’a cikin damuwa da rudani. Gwamnati na kira garesu da su guji irin wadannan ayukka da suka saba ma ka’idojin aikin jarida, musamman akan lamurran da suka shafi tsaro wadanda ke bukatar tantancewa.

Daga karshe, gwamna Matawalle ya mika godiya ga Shugaban Kasa ga irin kokarin da yake yi domin ganin an samu zaman lafiya a Jiharmu ta Zamfara. Haka kuma ina godiya ga al’umar Jiha dangane da irin addu’o’i da fatan alheri da suke yiwa wannan Jiha domin samun zaman lafiya. Ina ronkon Allah Madaukakin Sarki da Ya bamu zaman lafiya mai dorewa a wannan Jiha. Allah Ya taimake mu baki daya.

Post a Comment

0 Comments