Gwamnati Na Kashe Biliyan 120 Duk Wata Na Tallafin Man Fetur


Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya tabbatar da cewa gwamnatin na biyan naira biliyan 120 a kowanne wata a matsayin tallafin man fetur.

Mele Kyari ya fadi hakan ne a wani taro na musamman da ministoci ke yi wa manema labarai bayani a karo na biyar da aka gudanar a fadar gwamnatin Nijeriya dake Abuja.

Majiyarmu ta labarto cewa, Mele Kyari ya ce, a maimakon ƴan ƙasa su dinga sayen mai kan yadda farashin kuɗaɗen shigo da adana shi suke na naira 234 kan kowace lita guda, gwamnati na sayar da man a kan naira 162, don haka ita ke ɗaukan nauyin cikon kuɗin.

Sai dai ya ƙara da cewa, NNPC ba zai iya ci gaba da asarar waɗanan kuɗaɗe ba, don hakan ƴan Najeriya nan bada jimawa ba za su koma sayen man yada aka samo shi.

Ya kuma shaida cewa dole ne a bar kasuwa ta ƙayyade yada farashin mai zai kasance a ƙasar.

Post a Comment

0 Comments