Gwamnati Ta Ce Ta Cafke Mutum 18 Da Suke Daukar Nauyin Boko Haram


Daga Muhammad Farouk


Bayan shafe tsawon lokaci tana gwada kwanji, gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce ta fara bin masu samar da kudi ga kungiyar Boko Haram a kasar.

Ya zuwa yanzu dai akalla mutane 18 ne ke hannun jami'an tsaron Tarayyar Nijeriyar, wadanda ke binciken hanyoyin samar da kudi ga 'yan kungiyar Boko Haram. Gwamnatin kasar dai ta ce ta gano wasu kamfanonin canjin kudi da ke taka rawa wajen karbo kudin daga Hadaddiyar Daular Larabawa, tare da mika su ga 'yan ta'addan da ke ci gaba  da tayar da hankali a Nijeriya.

DW Hausa ta labarto cewa; da ma dai Hadaddiyar Daular Larabawan (UAE) ta yankewa kimanin 'yan canjin shida hukunci a shekarar da ta gabata, bayan samunsu da bai wa kungiyar ta Boko Haram kudi da suka kai akalla dalar Amurka dubu 782, baya ga sababin kamun da gwamnatin kasar ta ce tai nisa a binciken da ke shirin  bai wa 'yan kasar mamaki. Duk da cewar dai Abujar ba ta ambato sunaye  ko kuma kamfanonin canjin ba, tun a farkon wannan mako ne dai kungiyar 'yan canji ta kasar, ta bayyana cewar jami'an tsaron cikin gida wato DSS sun kame mata 'ya'ya.


Boko Haram na ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a Arewa maso Gabashin Najeriya
To sai dai kuma a fadar babban mashawarcin tsaron Tarayyar Najeriyar Janar Babagana Monguno gwamnatin kasar, na shirin durkusar da duk wasu  masu tunanin amfani dakudin  domin dakushe kokarin gwamnati na samar da zama lafiya tsakanin al'umma. Karkata zuwa ga masu samar da kudin tafi da harkoki na kungiyar dai, na zaman sabon babi a cikin yakin da ya shafe shekaru dai-dai har 12, amma kuma yafi mai da hankali zuwa ga karfi na hatsi.


Kama daga kudin na waje ya zuwa harajin cikin gida dai, kungiyar na kara fadada hanyoyin samun kudin shigar 'ya'yanta, abun kuma da ga dukkan alamu ke kara mata karfin tunkarar mahukuntan Najeriyar. To sai dai kuma a fadar Kabiru Adamu da ke zaman masanin harkar tsaro datse kudi ga kungiyar ta Boko Haram, na kara taimakawa ya zuwa kai 'yan dinkin hular zuwa gidan tarihi a lokaci kankani. Tun a shekara ta 2016 ne dai, kasar Hadaddiyar Daular Larabawan ta fara bin diddigin kudin kungiyar da ke badda sahu daga Turkiya, sannan ya kare a ofisoshin 'yan canjin a birane daban-daban cikin Tarayyar Nijeriyar.

Post a Comment

0 Comments