Gwamnati Za Ta Kashe 'Naira Biliyan 10' Wajen Rarraba Rigakafin Korona A Jihohi

 

Daga Wakilinmu 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta yi kasafin sama da naira biliyan 10 domin rarraba rigakafin korona zuwa jihohin ƙasar 36.

Majiyarmu ta Jaridar Punch ta labarto cewa ta ga daftarin kasafin kuɗin na rarraba rigakafin zuwa sassan Nijeriya. Kuma a cewar jaridar jihar Kano ce ke da kaso mai tsoka da kuɗin inda aka ware mata naira miliyan 685.4, yayin da Legas kuma inda cutar ta fi ƙamari aka ware mata naira miliyan 558.6 a matsayin kuɗaɗen rarraba rigakafin.

A cewar wata daftarin aiki da jaridar PUNCH ta gani, an kashe jarin naira biliyan 12.7 a matsayin kudin safara na allurar rigakafin, sayan kayayyakin PPE da na AEFI.

Post a Comment

0 Comments