Gwamnatin Kebbi Ta Yaba Ma Honarabul Kabir Tukura Kan Ayyukan Raya Kasa


Daga Abbakar Aleeyu Anache

Gwamnatin jihar kebbi karkashin jagorancin Sanata Atiku Bagudu, ta yabawa dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Zuru, Fakai, Danko Wasagu, da Sakaba, Honarabul Kabir Ibrahim Tukura a bisa namijin kokarin da yake yi na tabbatar da ayyukan raya kasa wadanda yake gudanarwa al'ummar mazabar shi. 

Gwamnatin ta nuna gamsuwa dangane da yadda Honarabul Kabir Ibrahim Tukura ya zuba kudi masu yawa wajen gina ayyuka masu matukar tasiri ga al'ummarsa. 

Honarabul Kabir Ibrahim Tukura ya dukufa matuka wajen ganin ya aiwatar da ayyukan ci gaba duba da yadda al'umma suke shan wahala. 

Dan majalisa Kabir Ibrahim ya yi alkawarin ci gaba da samarwa al'ummar da yake wakilta romon dimokuradiyya, musamman ababen more rayuwa da suke bukata tare da kai kudirorinsu a zauren majalisa. 

A cewar gwamnati ya zama wajibi gwamnati ta sanya ido kan nagarta da karkon ayyukan la'akari da alfanun da suke da shi ga al'ummar Zuru. 

Bayan haka Honarabul Kabir Ibrahim Tukura ya sha al'washin cewa zai cigaba da ba matasa fifiko wajen daukar nauyin su, domin samun ingantacceyar rayuwa tare da kuma jan hankalin su akan su guji aikata munanan ayyuka a cikin al'umma. 

Post a Comment

0 Comments